Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gabatar da rahoton bincike kan yadda kasashen Latin Amurka ke kallon kamfanonin Sin na shekarar 2019
2019-12-03 16:28:37        cri
A yau ne, aka gudanar da dandalin jin ra'ayoyin jama'a na shekarar 2019 a birnin Beijing, kan yadda kasashen waje ke kallon kamfanonin Sin, inda aka gabatar da rahoton bincike na wannan shekara, kan yadda kasashen Latin Amurka ke kallon kamfanonin Sin a hukunce.

An gudanar da binciken ne a kasashe 5 na Latin Amurka, wato Argentina, Brazil, Chile, Mexico da kuma Peru, inda aka ziyarci mutane 2500 wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu game da bunkasuwar tattalin arzikin Sin da ma yadda suke kallon mutuncin kamfanonin Sin.

Binciken da aka yi ya nuna cewa, kashi 73 cikin dari na adadin mutanen da aka tuntuba, sun bayyana cewa kamfanonin Sin na nuna halin ya kamata, adadin da ya zarce na kamfanonin Amurka, da Faransa. Kashi 80 cikin dari suna ganin cewa, dangantakar dake tsakanin kasashensu da kasar Sin na da muhimmanci matuka. A cikinsu, kashi 20 cikin dari suna ganin cewa, dangantakar ta fi muhimmanci. Mutane da aka tattauna da su sun nuna amincewa ga babban tasirin da tattalin arzikin Sin ya kawo wa bunkasuwar duniya da yankuna, kana sun nuna kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin. A ganinsu, raya shawarar "ziri daya da hanya daya" zai sa kaimi ga samun ci gaba a tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka, suna kuma fatan shawarar za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Latin Amurka a fannonin ayyukan more rayuwa, da tsara manufofi, da kuma cinikayya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China