Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gina tashar samar da lantarki daga hasken rana a sararin samaniya, ya zuwa 2035
2019-12-02 11:07:30        cri
Cibiyar nazarin fasahohin sararin samaniya CAST ta kasar Sin, ta ce kasar na shirin samar da tashar samar da lantarki daga hasken rana wadda karfinta zai kai matsayin megawatt a sararin samaniya, ya zuwa shekarar 2035.

Wani jami'in bincike na cibiyar CAST, Wang Li, ya ce tashar da za ta kasance a sararin samaniya, za ta rika samun makamashin rana da ba ya isowa ban kasa.

Jami'in ya bayyana haka ne yayin da yake halartar taro na 6 na kasar Sin da Rasha, kan aikin Injiniya, wanda ya gudana a makon da ya gabata a birnin Xiamen dake lardin Fujian na kudu maso gabashin kasar Sin.

Wang Li ya bayyana cewa, suna fatan karfafa hadin gwiwa da kasa da kasa domin samun nasarori a fannonin kimiyya da fasaha, ta yadda bil adama za su cimma burinsu na samu makamashi mai tsafta mara iyaka, nan bada dadewa ba.

Ya ce idan aka kwatanta da makamashin fetur, wanda aka yi ta amfani da shi kuma ya haifar da matsalolin muhalli, tashar ta sararin samaniya za ta fi inganci da dorewa, kuma za ta samar da wutar lantarki mai dorewa ga taurarin dan Adam da yankunan da annoba ta aukawa da kuma yankunan masu nisa a doron kasa.

Ya kara da cewa, bincike a wannan fanni, zai bunkasa ayyukan kirkire- kirkire da kimiyya a sararin samaniyar kasar, a fannin masana'antu masu tasowa, kamar na sufurin fasahohin sararin samaniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China