Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin finafinai na kasa da kasa karo na 2 a lardin Hainan na kasar Sin
2019-12-02 09:51:13        cri

An bude bikin finafinai na kasa da kasa karo na 2 na tsibirin Hainan a jiya Lahadi, a birnin Sanya dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.

Bikin na bana, ya samu jimilar masu neman shiga takarar samun lambar yabo ta Golden Coconut guda 1,495 daga kasashe 80, inda aka zabi finafinai da shirye-shiryen documentaries sama da 30 domin su yi takarar neman lambobin yabon.

Fitacciyar jarumar kasar Faransa Isabella Huppert, wadda ke shugabantar tawagar alkalai, ta ce kasar Sin na da dimbin albarkatun finafinai, kuma tana da hazikan masu bada umarni da masu shirya finafinai, haka zalika, tana da dadadden tarihi ta fuskar shirya finafinai.

A cewar kwamitin mashirya bikin, sama da finaifinai 200 daga kasashe da yankuna 61 za a tantance a rukunonin nune-nune 8 yayin bikin.

Bikin zai gudana ne har zuwa ranar 8 ga watan Disamban. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China