Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a wallafa bayanin da shugaba Xi Jinping ya rubuta game da tsare-tsaren siyasa da shari'a na kasar Sin
2019-11-30 16:13:55        cri
Mujallar "Qiushi" (wanda ke nufin "Neman Gaskiya") ta kasar Sin, za ta wallafa wani bayanin da babban magatakardan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping, ya rubuta, a ranar 1 ga watan Disamba mai zuwa. Bayanin da aka yiwa taken "Nacewa ga tsarin gurguzu da tsarin shari'a masu halayyar musamman ta kasar Sin, da kuma kokarin kyautata su".

Shugaba Xi ya bayyana a cikin bayaninsa cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana jagorantar al'ummun kasar, wajen gwajin manufofi daban daban, cikin shekaru 70 bayan kaddamar da jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, ta yadda sannu a hankali suka kafa tsare-tsare masu halayyar musamman ta kasar Sin, a fannonin siyasa da shari'a. Daga bisani an samu damar kare ci gaban al'ummar kasar Sin, tare da samar da fasahohi masu daraja a kokarin kyautata tsare-tsaren siyasa da na shari'a. A cewar shugaba Xi, kamata ya yi, daukacin 'ya'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, su yi imani da turbar da suka zaba wajen raya kasa, da tsayawa kan ra'ayoyi, da tsare-tsare, gami da al'adun kasar Sin. Da kuma ci gaba da kokarin raya kasar Sin, bisa manufofin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da jama'ar kasar suka gabatar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China