Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta tsawaita aikin tura ruwa domin kara yawan ruwan ga Yankunan Beijing da Tianjin da Hebei
2019-11-29 13:26:44        cri
An kaddamar da tsawaita aikin tura ruwa daga yankin kudu zuwa arewacin kasar Sin a birnin Linqing dake lardin Shandong na gabashin kasar, da nufin bunkasa samar da ruwa ga yankunan Beijin da Tianjin da Hebei.

A cewar Gao Bihua, ma'aikacin hukumar kula da hanyoyin ruwa na yankin gabashi, na aikin tura ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar, ya ce ana sa ran aikin da aka tsawaita ya samar da karin cubic mita miliyan 490 na ruwa zuwa yankunan Beijing da Tianjin da Hebei a kowacce shekara.

Jiang Xuguang, mataimakin ministan kula da albarkatun ruwa na kasar, ya ce da zarar an kamala, aikin zai saukaka hakar ruwa da ya zarce kima da inganta muhalli da samar da ruwa cikin gaggawa ga biranen dake yankin.

An tsara kamalla aikin sabbin hanyoyin ruwa dake gabashin hanyoyin da ake tura ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar ne a cikin watanni 21.

Tun bayan kammala kashin farko na aikin a yankunan gabashi da tsakiyar hanyoyin ruwan da suka tashi daga kudu zuwa arewa, sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa amfani da ruwa a yankunan dake kan hanyar, inda mutane sama da miliyan 100 suka ci gajiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China