Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An mayar da bakin haure 140 zuwa Chadi da Sudan daga Libya
2019-12-01 15:50:30        cri
Wata cibiyar tsugunar da bakin haure dake birnin Kurfa na kudancin Libya, ta sanar da tasa keyar bakin haure 140 zuwa kasashensu na asali.

Sanarwar da cibiyar ta fitar, ta ce an mayar da mutanen 140 ne zuwa kasashen Chadi da Sudan, bisa hadin gwiwar gwamnatocin kasashensu.

A cewar hukumar kula da batutuwan kaura ta duniya IOM, akwai sama da bakin haure 600,000 a Libya, wadanda galibinsu ke bukatar agaji, yayin da ake ci gaba da rikici a kasar.

Cibiyoyi a Libya na cike da dubban bakin haure da aka ceto daga teku ko kuma jami'an tsaro suka kama su, duk da kiran da al'ummomin duniya ke yi na a rufe cibiyoyin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China