Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kwashe 'yan gudun hijira 43 daga Libya zuwa Nijar
2019-11-29 20:15:18        cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta sanar a Jumma'ar nan cewa, ta kwashe 'yan gudun hijira 43 daga kasar Libya zuwa Jamhuriyar Nijar.

Hukumar ta wallafa a shafinta na tweeter a safiyar yau cewa, 'yan gudun hijirar sun isa Nijar lami lafiya, kuma su ne na baya-bayan da hukumar ta kwashe daga kasar ta Libya karkashin shirinta na jin kai, inda ake sa ran tsugunar da su a kasar Swizerland a wani lokaci. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China