Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara inganta muhallin kasuwanci
2019-11-28 10:30:16        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bukaci a dauki kwararan matakan aiwatar da dokar kyautata yanayin kasuwanci domin kara samar da ingantaccen muhallin kasuwanci karkashin tsarin mutunta dokokin ciniki.

A wata sanarwar da aka fitar bayan kammala taron majalisar gudanarwa ta kasar na wannan makon wanda firaminista Li ya jagoranta, an ce, ya kamata a kara kokari wajen warware dukkannin matsalolin dake shafar bangarorin harkokin kasuwanci da ayyukan zuba jari.

Majalisar gudanarwar Sin ta sanar da jama'a wasu dokokin da suka shafi kyautata muhallin kasuwanci, wadanda zasu fara aiki daga ranar 1 ga watan Janaiirun 2020.

A cewar sanarwar, inganta muhallin kasuwanci zai taimaka matuka wajen kyautata aikin samar da kayayyaki, da bunkasa yin takara, kuma shi ne ingantaccen matakin da zai kyautata yanayin ciniki, da daidaita yanayin tunanin al'umma, kuma zai iya jurewa dukkan wani matsin lamba, kana zai tabbatar da samun bunkasuwa da samar da guraban ayyukan dogaro da kai. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China