Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban Bankin Duniya
2019-11-21 11:02:45        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban bankin duniya, David Malpass, inda ya bayyana kudurin kara zurfafa hadin gwiwar kasar Sin da Bankin duniya a muhimman bangarori.

Li Keqiang ya ce bankin duniya muhimmiyar cibiyar hadin gwiwa ce a duniya, kuma kasar Sin na ba da muhimmanci sosai ga raya dangantakarta da bankin, sannan a shirye take ta zurfafa hadin gwiwarsu a muhimman fannoni kamar na kare muhalli, da rayuwar mabanbantan halittu, da yaki da talauci, ta hanyar hadin gwiwa a fannonin kudi da kwararru.

Haka zalika, ya ce kasar Sin za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, wajen hada hannu domin ci gaban duniya.

A nasa bangaren, David Malpass, ya ce tattalin arzikin duniya a yanzu na fuskantar kalubale da dama dake bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su magancesu.

Ya ce tattalin arzikin kasar Sin na da karfi sosai, kuma kasar ta samu nasarorin bisa aiwatar da maufar bude kofa, yana mai cewa gwamnatin Kasar Sin na namijin kokari a fannonin ci gaban tattalin arziki da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kare muhalli, kuma a shirye Bankin Duniya yake ya zurfafa hadin gwiwarsa da kasar Sin a wadancan bangarori. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China