2019-11-20 13:57:50 cri |
Wata sanarwa da hukumar CRRC, daya daga cikin masu hannayanen jarin asusun a kasuwar hannayen jarin Shanghai, ta bayyana cewa, jarin asusn ya kai Yuan biliyan 147.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 21.02.
Sanarwar ta ce, asusun zai juba jari ne a fannonin masana'antun da suka shafi sabbin kayayyaki, da sabbin fasahohin bayanan sadarwa na zamani da kayayyaki laturoni.
Kasar Sin dai ta fitar da wasu kwararan matakai na hanzarta daga matsayin bangaren masana'antun samar da kayayyakin kasar, da nufin kara samar da kayayyaki masu inganci.
A hannu guda kuma, mahukuntan kasar, sun fitar da wasu ka'idoji, don kara bunkasa wannan sashe, da bangaren samar da hidima na zamani, da wani shiri na shekaru 4 kan yadda za a kara karfin aikin tsara kayayyakin kasar.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China