Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yiwa manyan kamfanonin kera jiragen ruwa biyu na kasar Sin garambawul
2019-11-26 15:44:01        cri

An kafa babban rukunin kera jiragen ruwa ta kasar Sin a yau Talata 26 ga wata, matakin da ya nuna cewa, an kammala aikin yiwa kamfanonin kera jiragen ruwa mafi girma biyu a kasar Sin garambawul, wanda kuma ya alamta cewa, rukunin kera jiragen ruwa ta kasar Sin da aka kafa ta zama irinsa mafi girma a duniya wajen kera jiragen ruwa.

Wannan rukunin da aka kafa ta hada tsohon kamfanin CSSC da ma kamfanin CSIC waje guda. Wadda ta kunshi cibiyoyin nazari, kamfanoni da kuma kamfanonin dake sayar da hannayen jari a kasuwa da yawansu ya kai 147, yawan dukiyoyin mallakar rukunin ya kai RMB Yuan biliyan 790, inda take da ma'aikata dubu 310.

Sakataren kwamitin jam'iyyar JKS na rukunin kana shugaban hukumar zartarwar rukunin, Lei Fanpei ya nuna cewa, kafuwar wannan rukunin mataki ne da zai kara karfin kasar Sin a fannin teku, kere-kere da ma kimiya da fasaha, wanda kuma zai sa kaimi ga bunkasuwar masana'antun tsaron kasar da yi wa kamfanonin jarin kasar gyaran fuska, da kuma daga karfin takarar kasar Sin a duniya ta fuskar masana'antun kera jiragen ruwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China