Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Afrika sun nemi a hada hannu wajen kawar da bambancin jinsi a nahiyar
2019-11-26 11:33:41        cri

An kaddamar da taro karo na 4 kan daidaiton jinsi, jiya Litinin a birnin Kigali na Rwanda, inda shugabannin Afrika suka nemi a hada hannu wajen cike gibin dake akwai tsakanin jinsuna a nahiyar.

Wannan ne karo na farko da taron da ake yi bayan shekaru bibbiyu ke gudana a Afrika, bayan wadanda aka yi a kasashen Turkiyya da Philippines da kuma Amurka.

A cewar ma'aikatar kula da jinsi ta Rwanda, taron karon farko a Afrika, ya gabatar da wata dama ta bayyana ayyukan da aka yi a nahiyar wajen inganta daidaiton jinsi da karfafa gwiwar mata da kuma samun goyon bayan abokan hulda wajen gaggauta ganin tasirin aikin.

Taken taron na yini 3 shi ne, "kawar da abubuwan dake tarnaki ga tabbatar da daidaiton jinsi", wanda ya hada wakilai sama da 2,000, ciki har da shugabannin kasashe da abokan hulda da kungiyoyi da kuma malamai.

A jawabinta, Shugabar Habasha, Sahle-Work Zewde, ta ce cimma daidaiton jinsi a Afrika na bukatar yunkuri mai karfi da hadin gwiwa, tana mai cewa idan har ba a damawa da mata, to ba za a taba samun ci gaba ko Afrikar da ake buri ba. Ta ce akwai bukatar tabbatar da dukkan hukumomi na tabbatar da daidaiton jinsi, sannan shirye-shirye da manufofi da gangami su rika nuna daidaiton jinsi.

A nasa bangaren, shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamt cewa ya yi, idan ana son cimma daidato tsakanin jinsuna, to kamata ya yi kasashe su magance abubuwan dake hana mata da 'yan mata samun damarmakin ilimi da aikin yi da kudi da shiga siyasa, daidai da takwarorinsu maza. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China