Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa sabon dandalin nazarin ilmin kimiyya na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2019-10-09 14:52:16        cri

Cibiyar hadin gwiwa ta nazarin harkokin ilmin kimiyya tsakanin Sin da Afirka dake jami'ar kimiyya da fasahar aikin gona ta Jomo Kenytta dake arewacin birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya, ita ce irinta na farko da gwamnatin kasar Sin ta kafa a ketare, wadda ta kasance muhimmin dandalin hadin gwiwa ta yin nazari kan ilmin kimiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Maryam ta nazarci ayyukan wannan cibiya ga kuma karin bayaninta……

A shekarar 2013, aka kafa wannan cibiya ta nazarin ilmin kimiyya bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, wadda ta samu goyon baya daga hukumomin kimiyya da fasaha na kasar Sin guda 18. Ya zuwa yanzu, cibiyar ta riga ta kafa dangantakar hadin gwiwa da hukumomin kimiyya da fasaha guda 20 dake kasashen Kenya, Tanzaniya da kuma Habasha da sauransu. Shugaban cibiyar Yan Xue ya yi bayanin cewa, cibiyar tana gudanar da ayyukan nazari kan fannoni daban daban dake shafar muhimman batutuwan da kasashen Afirka suke fuskanta. Ya ce, "Da farko, nazarin da muke yi ya shafi kare halittu, wadanda suka hada da dabobbi, tsirrai da kuma kananan halittu. Na biyu kuma, muna gudanar da nazari kan muhalli, musamman ma a fannin kiyaye albarkatun ruwa da kuma yin amfani da albarkatun ruwa yadda ya kamata. Sa'an nan, na uku shi ne, nazari kan ayyukan gona na zamani. A karshe kuma, nazari game da tsarin labarin kasa, watau yin hasashe kan yawan hatsi da wadannan kasashe za su iya samarwa, da kuma samar da labarai game da tsarin albarkatun ruwa na kasashen. Bugu da kari, cibiyar ta kuma kula da harkokin tarbiyya, ya zuwa yanzu, ta riga ta karbi dalibai na kasar Kenya guda 210."

Samun isasshen hatsi shi ne mihimmin batu dake jan hankulan kasashen Afirka, musamman ma kasar Kenya wadda take samun karuwar yawan al'umma da sauri. Cibiyar hadin gwiwar ta yin nazari kan ilmin kimiyya dake tsakanin Sin da Afirka ta kafa yankin gona mai muraba'in mita dubu 13 a yankin Mwea na kasar Kenya, domin yin gwaje-gwaje kan shuka amfanin gona masu kyau. Haka kuma, ta cimma nasarar samun wani iri shinkafa, wanda ya dace da muhallin kasar Kenya. Mai kula da harkokin gona na wannan cibiya Liu Fan ya yi bayanin cewa, "A kasar Kenya, su kan samar da shinkafa kimanin kilo 4500 cikin hekta 1. Amma a kasar Sin, muna iya samar da shinkafa kilo dubu 15. Kana, bisa gwaje-gwajen da muka yi da irin shinkafa da muka kawo nan, yanzu muna iya samar da shinkafa kilo dubu 10.5 cikin hekta 1. Ma'anar ita ce, muna iya yin amfani da wannan irin shinkafa wajen taimakawa kasar Kenya kan samar da karin shinkafa."

A sa'i daya kuma, sakamakon da cibiyar ta samu sun riga sun fara taimakawa al'ummomin kasar Kenya. A watan Mayu na shekarar 2018, madatsar ruwa ta Patel Dam ta rushe, lamarin da ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama. Bayan aukuwar hadarin, cibiyar ta yi nazari kan labarin wurin, da kuma gabatar da sakamakon da ta samu ga gwamnatin kasar.

Ban da haka kuma, masanan Sin da Kenya sun rubuta littafi mai taken "Tsirran kasar Kenya", da kuma kafa yankin tsirran magunguna na kasar Kenya. Kana, an riga an fara amfani da sayar da magungunan da wadannan masana suka fitar daga wannan yanki. A halin yanzu kuma, sun dukufa wajen rubuta wani littafi mai taken "Bayani kan dabbobin gandun daji a kasar Kenya". Yan Xue ya ce, "Kimiyya da fasaha shi ne babban tushen samar da kayayyaki, sakamakon da aka samu sun haifar da sabbin sana'o'i a wannan kasa da kuma kara kudin shiga da fararen hular kasa za su samu cikin gajeren lokaci."

Cikin shekaru 6 da suka gabata, cibiyar hadin gwiwar ta yin nazari kan ilmin kimiyya na Sin da Afirka da aka kafa a kasar Kenya ta sami babban ci gaba, ta kuma fara hadin gwiwa da kasashen Tanzaniya, Madagascar da kuma Habasha ta yanar gizo. Tana kuma yin hadin gwiwa da jami'o'i da hukumomin kimiyya da fasaha kimanin 20 dake kasashen Afirka sama da guda 10 cikin dogon lokaci.

Dangane da sakamakon da cibiyar ta samu, shugaban cibiyar na bangaren Afirka Robert Gituru ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana da fasahohi da dama wajen raya harkokin tsirrai da warware matsalolin da bil Adama suke fuskanta. Kuma hadin gwiwar da masanan Sin da Afirka suka yi a wannan cibiya ya taimakawa al'ummomin kasar Kenya wajen kyautata zaman rayuwarsu, har ma ga dukkan mutanen duniya baki daya." (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China