Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka na sa ran kyautata hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin ta fuskar tsaro
2019-07-17 14:57:54        cri

Ana gudanar da taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka karo na farko a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, wanda babban taken taron shi ne yin hadin gwiwa wajen inganta harkokin tsaro. Manyan wakilai kusan dari 1 daga kasashe 50 na Afirka da hukumomin harkokin tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da wakilan rundunar askarawan kasar Sin sun tattauna yadda za a kara yin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin Sin da Afirka ta fuskar zaman lafiya da tsaro. Wasu wakilan kasashen Afirka sun nuna fatansu kan hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin 2 a nan gaba.

Smail Chergui, jami'in AU mai kula da zaman lafiya da tsaro ya nuna cewa, ta'addanci yana daya daga cikin manyan barazanar da nahiyar Afirka take fuskanta ta fuskar tsaro. Kasar Sin, abokiyar Afirka ce da ake girmamawa wajen yin hadin gwiwa. Kungiyar AU tana son inganta hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannin tsaro."Ana girmama kasar Sin sosai a nahiyar Afirka wajen hada kai da ita. Mun kara sanin dankon zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka ne bayan ganin shugabannin kasashen Afirka da yawa sun halarci taron kolin Beijing na FOCAC a bara, lamarin da ya karfafa zuciyarmu kan hadin gwiwar Sin da Afirka. Don haka 'yan Afirka za mu kyautata hadin gwiwa da Sin a fannonin tsaro da raya kasa."

Hahya Ould Hademine, ministan tsaron kasar Mauritania ya gode wa kasar Sin da shirya wannan taron dandali. A cewarsa, yanzu ana fuskantar babbar sauyi a duniya baki daya. Kokarin da kasar Sin da kasashen Afirka suke yi ta fuskar inganta tsaro zai taimaka wa 'yan Afirka samun adalci da yin zaman daidai wa daida. "Kowa na sane da cewa, kasar Sin na himmantuwa wajen yin zaman daidai wa daida da sauran kasashen duniya ba tare da wani sharadi ba. Amma kasashen yammacin duniya sun hada kai da kasashen Afirka ta fuskar tsaro bisa wasu sharudda. Yadda kasar Sin take yi ya kawo wa kowa alheri, yana amfanar dukkan sassa masu ruwa da tsaki. A ganina, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaro, kamar yadda take taka muhimmiyar rawa ta fuskar tattalin arziki da aikin soja a duniya."

Alain Fortunet Nouatin, ministan tsaron kasar Benin ya nuna fatansa na ganin kasar Sin da kasashen Afirka sun kara hada kansu a fannoni da dama a nan gaba. "Da farko akwai wasu fannoni da za mu iya kyautata hadin gwiwarsu, alal misali, fannonin tattara bayanai, dabarun yaki, da injuna. Muna bukatar karin fasahohin tattara bayanai, wadanda suke kawo wa tsaron kasa barazana, a kokarin daukar matakan yin rigakafi. Na biyu kuma, muna bukatar karin taimako ta fuskar injuna. Na uku muna fatan kara samun taimako da tabbaci wajen tabbatar da tsaron teku, a kokarin tabbatar da tsaron zirga-zirga da sufuri a teku, musamman ma a yankin gaabar tekun Guinea."

Taluva David Tamba Ocil, mataimakin hafsan hafsoshin rundunar kasar Saliyo ya yi bayani da cewa, wasu kungiyoyin kasa da kasa su kan shawarci kasashen Afirka da su rage kudin da suke kashewa ta fuskar tsaron kasa da kuma rage yawan sojoji don rage kudin da gwamnati ke kashewa, amma idan kasashen Afirka sun fuskanci barazanar tsaro, wadannan kasashe ba sa samar da taimako. Kasar Sin kuwa, abokiyar Afirka ce mai aminci. Yana fatan za a inganta hadin kai da kasar Sin wajen kyautata karfin tsaron kasa, a kokarin kara kiyaye albarkatun halittu da kyautata zaman rayuwar jama'a. "Wasu kasashen Afirka ba su da isasshen karfin kiyaye ikon mulkin kansu da kuma albarkatun halittunsu, lamarin da ya sanya kasashe masu fama da talauci ke kara fama da kangin talauci, saboda ba su iya kiyaye albarkatunsu yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, wasu kasashe suna da iyakar kasa mai tsawo tsakaninsu da sauran kasashe, amma ba su da isasshen karfin yaki da wadanda suka shiga kasa ba bisa doka ba. Har ila yau kuma, wasu kasashen Afirka ba sa iya tabbatar da tsaro kan intanet, ba sa iya daidaita barazanar da ta'addanci yake haifarwa. Idan kasar Sin ta taimaka wa kasashen Afirka wajen kyautata karfinsu ta fuskar tsaro, za a amfana sosai wajen kiyaye albarkatun halittu, da kara azama kan ci gaban kasa." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China