Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matasan Afirka sun nuna yabo ga tsarin siyasa na kasar Sin
2019-09-05 14:42:25        cri

A jiya ne, aka rufe bikin haduwar matasan Sin da Afirka karo na 4 mai taken "tsara burin matasa don samar da sabon yanayin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka" a birnin Guangzhou na kasar Sin, inda matasa 95 daga kasashen Afirka 51 sun gano al'adun gargajiya, da fasahohin zamani, da bunkasuwar zamantakewar al'umma, da tsarin siyasa na kasar Sin, dukkansu sun nuna yabo ga tsarin siyasa na kasar Sin, tare da yanayin zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasar.

Sakataren kula da harkokin waje na jam'iyyar kawancen demokuradiyya ta kasar Nijer Mamane Garba ya bayyana cewa, a matsayin memban jam'iyya, a ganinsa tsarin siyasa mai kyau zai tabbatar da bunkasuwar kasar Sin daga tushe. Ya ce,  

"Tsarin siyasa da shugaba Xi Jinping ke aiwatarwa ya tabbatar da bunkasuwar kasar Sin."

Malam Garba ya kara da cewa, idan ba a kawar da talauci ba, da wannan kasa ba za ta kasance kasa mai ci gaba ba. Tsarin gurguzu mai alamar Sin na sabon zamani ya fi dora muhimmanci ga masu fama da talauci da taimaka musu wajen kawar da talauci, idan aka kwatanta shi da sauran tsarin siyasa na duniya. Musamman ya yi bayani game da misali na kauyen Lianzhang na garin Lianjiangkou dake birnin Yingde na lardin Guangdong, ya ce, an sa kaimi ga mazauna kauyen wajen kara kudin shiga da kawar da talauci ta hanyar jawo ayyukan zuba jari da raya sha'anin noma na zamani da sha'anin kera kayayyaki, kuma gwamnatin kauyen ta soke buga haraji gare su, wadannan matakan kawar da talauci suna da amfani.

Mai ba da taimako na musamman ga shugaban jam'iyyar APC dake kan karagar mulkin kasar Nijeriya Eromosele Ehigie Daniel shi ma ya nuna yabo ga kauyen Lianzhang, ya ce,

"Ya kamata shugabannin siyasa su taimaka wajen kyautata zaman rayuwar jama'a. Na ga shugabannin karamar gwamnatin kauyen kasar Sin sun yi kokarin jawo jarin waje, da taimakawa mazauna kauyen wajen samar da kayayyaki da sayar da su ta yanar gizo. Wannan ya shaida cewa, burin gwamnatin kauye shi ne taimakawa jama'a wajen kyautata zaman rayuwarsu."

Kana mista Daniel ya bayyana cewa, ya ga bisa tsarin gurguzu mai alamar Sin na sabon zamani, jama'ar kasar Sin sun zama mai kyau, kuma an bunkasa tattalin arziki, da al'adu, da ba da ilmi, da kimiyya da fasaha da sauransu, wadanda suka shaida cewa, wannan tsari ya dace da yanayin kasar Sin.

Game da ma'anar bikin haduwar matasan Sin da Afirka a wannan karo, Daniel yana ganin cewa, shirya wannan biki ya shaida tunanin hangen nesa na shugabannin kasar Sin. Ya ce,

"An shuka iri, sai ya girma da ganin amfaninsa. Matasan Sin da Afirka sun yi mu'amala da koyi da juna don bunkasa da zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a nan gaba."

Daniel ya kara da cewa, a halin yanzu, akwai yanayin nuna bambanci ga mutane domin launin fata da harsuna. Amma a wannan karo, ya zo kasar Sin ya ga sahihanci da sada zumunta da amincewa da juna na Sinawa. Ko da yake akwai bambanci kan launin fata da harsuwa da kuma al'adu, amma ya ji farin ciki a nan domin an nuna amincewa da juna. Ya ce, zai yi kokarin samar da gudummawa wajen kara sada zumunta da sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China