Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kai harin boma-bomai ga wurin dake dab da ofishin jakadancin Amurka dake kasar Iraki
2019-09-24 11:14:18        cri
Jami'in tsaron kasar Iraki ya bayyana a jiya cewa, an kai harin boma-bomai biyu a wani wurin dake dab da ofishin jakadancin Amurka dake birnin Bagadaza na kasar Iraki, sai dai babu wanda ya ji rauni a sakamakon harin.

Bayan abkuwar harin, an kunna jiniya don yin kashedi ga jama'a a yankin mai cike da zaman lafiya, da kara daukar matakan tabbatar da tsaro.

Mazaunan wurin sun bayyana cewa, sun ji fashewar boma-bomai a cikin yankin zaman lafiya.

Yankin yana tsakiyar birnin Bagadaza, kuma hukumomin gwamnatin kasar Iraki da ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya dake kasar suna cikin wannan yanki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China