Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 74 a zanga-zangar masu kin jinin gwamnati a Iraqi
2019-10-28 11:03:42        cri

Hukumomi a kasar Iraqi sun sanar a jiya Lahadi cewa adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar gangamin masu bore da ya barke a fadin kasar don nuna adawa game da matsalolin rashin aikin yi, da rashawa, da kuma karancin kyawawan hidimomin zaman rayuwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 74 kana wasu mutanen sama da 3,600 sun samu raunuka.

Ali al-Bayati, mamba a hukumar kare hakkin dan adam mai zaman kanta ta kasar Iraqi (IHCHR), ya fada cikin watan sanarwa cewa, an samu barkewar tashin hankali ne tsakanin masu zanga zanga da jami'an tsaro daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Oktoba, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayuka 74.

Ya ce galibin mutanen da suka mutu an harbe su ne da harsasai daga jami'an tsaron jam'iyyun siyasa a lokacin da masu zanga zangar suka yi yunkurin kutsawa helkwatar jam'iyyun, bugu da kari kuma jami'an tsaron sun kuma yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu boren.

Al-Bayati ya kara da cewa, masu zanga zangar gami da jami'an tsaron kimanin 3,654 ne suka samu raunuka, galibinsu a sanadiyyar hayaki mai sa hawayen.

A lokacin zanga zangar ta tsawon kwanaki uku, sama da gine-ginen gwamnati, da helkwatocin jam'iyyun siyasa, da wasu gine-ginen 'yan kasuwa 90 ne wasu daidaikun mutane suka cinnawa wuta da nufin sauya zanga zangar ta lumana zuwa ta tashin hankali, in ji sanarwar.

A cewar al-Bayati, jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, da ruwan zafi, da bam mai kara, da nufin tarwatsa gungun masu zanga zangar a lokacin da suke artabu da jami'an tsaron a birnin Bagadaza da sauran lardunan kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China