Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan tsaron kasar Amurka ya ce sojojin kasar ba za su tsaya a Iraki ba
2019-10-24 14:25:47        cri
Ministan tsaron kasar Amurka, Mark Esper, ya ziyarci kasar Iraki a jiya Laraba, inda ya gana da firaministan kasar Iraki, Adel Abdul Mahdi, gami da bayyana masa cewa, ba za a jibge sojojin kasar Amurka kimanin 1000, da suka janye jiki daga kasar Syria, a kasar Iraki ba.

Ofishin firaministan kasar Iraki ya fadi haka cikin wata sanarwar da ya gabatar, haka kuma ya ce yayin da suke ganawar, jami'an biyu sun tattauna batutuwan da suka hada da huldar dake tsakanin Iraki da Amurka, da yunkurinsu na ci gaba da hadin gwiwa domin dakile kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, da yanayin da kasar Syria ke ciki, da dai makamantansu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China