Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da bada gudummawarta wajen farfado da Iraki
2019-08-29 11:38:32        cri
Zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin a MDD, Wu Haitao a jiya Laraba ya bayyana cewa, a karkashin tsarin "ziri daya da hanya daya" ne kasar Sin za ta ci gaba da bada gudummawarta wajen farfado da kasar Iraki ta fannonin makamashi da manyan ayyuka, kuma za ta bada taimako gwargwadon karfinta wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a kasar ta Iraki.

A gun taron kwamitin sulhu da aka gudanar a wannan rana dangane da batun Iraki, Mr. Wu Haitao ya bayyana cewa, Sin na nuna goyon baya ga duk wani kokarin da ake yi na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma yaki da ta'addanci a Iraki, kuma tana nuna goyon bayanta ga tawagar MDD ta tallafawa Iraki don ta ci gaba da gudanar da aikinta.

Wu Haitao ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su ci gaba da goyon bayan Iraki wajen inganta nasarorin da ta samu wajen yaki da ta'addanci da kiyaye tsaron kasa. Kamata ya yi kasa da kasa su cika alkawuranta, kuma su ci gaba da samar da tallafi ga Iraki, don ta gano wata hanyar da ta dace ta bi domin samun ci gabanta.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China