Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Moussa Faki ya bayyana matukar jimamin aukuwar zaftarewar kasa a Kenya
2019-11-25 09:18:12        cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar kaduwa, bayan samun labarin zaftarewar kasa a gundumar West Pokot dake arewa maso yammacin kasar Kenya, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 37.

Mahamat ya bayyana jimamin aukuwar wannan lamari ne ta shafin sa na twitter a jiya Lahadi. Ya ce wannan lamari ya auku, jim kadan bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar da ambaliyar ruwa mai tsanani, a yankunan kasashen Sudan ta Kudu, da Tanzania, da Congo Brazzaville, da janhuriyar Afirka ta tsakiya, da Somalia da kuma Habasha.

Rahotanni sun ce zaftarewar kasar ta Kenya, ta biyo bayan mamakon ruwan sama ne da aka kwashe tsawon lokaci ana yi, inda a daren Juma'a ya haifar da wannan ibtila'i.

Tuni dai shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda wannan ibtila'i ya aukawa, yana mai tabbatar da cewa, za a tabbatar da gano daukacin wadanda suka bace, tare da daukar karin matakan kare rayukan jama'a, sanadiyyar aukuwar wannan annoba a nan gaba.

Zaftarewar kasa ta riga ta haifar da yanayin jin kai, a kauyukan gundumar West Pokot dake makwaftaka da kasar Uganda, da Sudan ta kudu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China