Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin dashen itatuwa na Sin ya samu babbar lambar yabo ta MDD
2019-09-19 20:01:39        cri

Shirin dashen itatuwa mai lakabin "Ant Forest" a Turance, wanda ke gudana karkashin kulawar kamfanin cinikayya ta yanar gizo na Alipay dake nan kasar Sin, ya lashe lambar yabo mafi girma ta hukumar kare muhalli ta MDD ko UNEP a takaice.

Shirin "Ant Forest" wanda ke samun tallafi daga kungiyoyin kula da muhalli masu zaman kan su daban daban, ya lashe lambar yabon ta UNEP ta bana, sakamakon irin tasirin sa na kawar da barazanar kwararar hamada a wasu sassan kasar Sin.

A Alhamis din nan ne dai hukumar ta UNEP ta fitar da wata sanarwa a ofishin ta dake birnin Nairobin kasar Kenya. Sanarwar dake cewa shirin "Ant Forest", ya aiwatar da kudurin mutane da yawansu ya kai miliyan dari biyar, na shuka itatuwa a sassan kasar Sin masu fuskantar barazanar hamada.

Tun kaddamar da shirin a watan Agustan shekarar 2016, "Ant Forest", tare da sauran abokan huldar sa, sun shuka bishiyoyi kusan miliyan 122, a yankunan da suka hada da Mongolia ta gida, da lardunan Gansu, da Qinghai da kuma Shanxi. Wadannan itatuwa sun karade filin da fadin sa ya kai hekta 112,000, dashen itatuwan da ya kasance mafi girma da sassa masu zaman kan su suka taba gudanarwa a fadin kasar.

Cikin sanarwar da aka fitar, babban daraktan UNEP Inger Andersen, ya ce hadin gwiwar "Alipay da shirin "Ant Forest", ya nuna irin yadda fasahohin zamani ke iya sauya duniya, ta hanyar ba da damar ci gajiya daga makamashi mai nagarta, da kirkire kirkire da al'ummun duniya ke aiwatarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China