Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Xi da shugaban Kenya sun gana kan karfafa dangantaka
2019-09-05 09:40:46        cri

Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Yang Jiechi, ya tattauna da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a ranar Laraba game da batun karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Yang, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), kana daraktan ofishin dake kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiya na CPC, ya isar da sakon gaisuwar shugaba Xi ga Kenyatta, ya ce muhimman tarukan ganawa da aka gudanar a shekarun baya bayan nan tsakanin shugabannin biyu, sun haifar da kyakkyawan sakamako wajen daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi.

Ya ce, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da taimakawa kasar Kenya domin ta cimma burinta na manyan ajandodinta hudu nan da shekarar 2030, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya (BRI), kana ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a Beijing.

A nasa bangaren, Kenyatta ya bukaci Yang ya isar da sakon gaisuwarsa zuwa ga shugaba Xi, kana ya godewa kasar Sin saboda irin taimakon da take baiwa kasar Kenya wajen bunkasa tattalin arzikinta da kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummarta.

Da yake nuna yabo game da saurin bunkasuwar hadin gwiwar dake tsakaninsu, Kenyatta ya ce, kasar Kenya da kasashen Afrika a shirye suke su yi aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da muhimman kudurorin da aka cimma matsaya kansu a lokacin taron kolin FOCAC na Beijing, da kuma kara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin bangarorin a dukkan fannoni. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China