Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya samu lambar yabo na Nobel
2019-10-12 16:47:07        cri

Kwamitin bayar da lambar yabo ta Nobel na The Norwegian Nobel Committee, ya sanar da Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, a matsayin wanda ya samu lambar yabo na zaman lafiya na Nobel, saboda kokarinsa na warware rikicin iyakar kasar da makwabciyarta Eritrea.

Shugabar kwamitin Berit Resis-Andersen ce ta sanar da haka a Oslo, inda ta ce a lokacin da Abiy Ahmed ya zama firaminista a watan Afrilun 2018, ya bayyana cewa yana fatan komawa tattaunawa da Eritrea. Bisa hada hannu da Isaias Afwerki, Shugaban Eritrea, Abiy Ahmed ya gaggauta shirya ka'idojin yarjejeniyar kawo karshen dadaddiyar zaman doya da manjan da ake tsakanin kasahen 2.

Berit Reiss-Anderson, ta ce Abiy Ahmed ya kuma kaddamar da muhimman gyare-gyare a Habasha domin kyautata rayuwar al'ummar kasar. Ya kuma fitar da kasar daga yanayin ta baci da janye sojoji da kuma fareren hula da ake zargi da cin hanci, tare da daga matsayin mata a harkar siyasa.

Ta kara da cewa, yana kuma aiki wajen tabbatar da tsarin zaman lafiya da sulhu a yankin gabashi da arewa maso gabashin Afrika.

Har ila yau, ta kuma shaidawa manema labarai cewa kwamitin na sa ran Abiy Ahmed zai ci gaba da kokarinsa na samar da zaman lafiya da sulhu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China