Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afirka da su yi kokarin magance yadda ake tilastawa mutane barin gidajensu
2019-11-07 09:47:47        cri

Kungiyar tarayyar Afirka(AU) ta yi kira ga kasashen nahiyar, da su kara zage damtse wajen ganin sun magance yadda ake tilastawa mutane barin matsugunansu, su kuma yi amfani da yarjejeniyar kula da 'yan gudun hijira da kaurar jama'a ta duniya.

Kungiyar wadda ta jaddada hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba, ta ce, sama da kaso 1 bisa uku na mutanen da aka tilastawa barin muhallansu, suna zaune ne a kasashen nahiyar. Wannan adadi ya kunshi 'yan gudun hijra miliyan 6.3 da masu neman mafaka miliyan 14.5 dake zaune a sansanonin tsugunar da 'yan gudun hijira, lamarin da kungiyar ta ce, wajibi ne kasashen nahiyar su kara kaimi wajen magance wadannan matsaloli.

A cewar kungiyar, amfani da yarjejeniyar da duniya ta lamunta da ita, ya nuna yadda a baya-bayan nan duniya ta karkata wajen sanya batun 'yan gudun hijira da masu neman makafa, da wadanda suka rasa matsugunansu da masu kaura a cikin manyan manufofi da ake tattaunawa a Afirka da ma duniya baki daya.

Kungiyar ta yi wannan kira ne gaggawa yayin taron manyan jagororin kungiyar game da 'yan gudun hijira da masu kaura da wadanda aka raba da matsugunansu da aka bude tun ranar 4 har zuwa 8 ga watan Nuwanba a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Taken taron dai shi ne "Shekarar 'yan gudun hijira, da wadanda suka koma gida da wadanda suka rasa muhallansu: Yadda za a magance matsalar tilastawa mutane barin muhallansu a Afirka". Ana sa ran taron ya duba tare da ba da shawara kan muhimman manufofi da dokokin da suka wajaba a dauka a bangaren kaurar jama'a, da 'yan gudun hijira da ma wadanda aka tilastawa barin muhallansu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China