Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin amfani da batun HK don tsoma baki cikin harkokin kasar Sin zai ci tura
2019-11-23 20:46:01        cri

A kwanakin baya ne majalisar dokokin Amurka ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong na shekara ta 2019, inda aka jirkita gaskiya da nuna goyon-baya ga masu tada kayar baya da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan Hong Kong, al'amarin da ya bayyana irin makircin da wasu mutanen Amurka suka kulla na kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Babu tantama irin wannan yunkuri zai sha kaye.

Na farko, tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong da Amurka ta yi, zai fadakar da jama'a kan cewa, abun da ya fi muhimmanci shi ne kwantar da tarzoma da farfado da zaman doka da oda a wajen. Na biyu, lalata zaman doka da oda a Hong Kong zai kawo babbar illa ga moriyar kamfanonin kasa da kasa ciki har da na Amurka. Na uku shi ne, zartas da shirin doka kan Hong Kong da Amurka ta yi ya sabawa dokoki gami da ka'idojin kasa da kasa.

Harkokin yankin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda bai kamata wasu kasashe su tsoma baki ciki ba.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China