Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba za a cimma yunkurin tsoma baki cikin harkokin kasar Sin ba
2019-11-20 19:16:02        cri

A yau Laraba ne gidan rediyon kasar Sin, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Ko shakka babu ba za a cimma yunkurin tsoma baki a cikin harkokin kasar Sin ba", inda aka bayyana cewa, a jiya 19 ga wata, majalisar dattijai ta Amurka, ta zartas da wata doka kan hakkin dan Adam da demokuradiya a yankin Hong Kong, matakin da ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ka'idar tushe dake shafar hulda tsakanin kasa da kasa.

Makasudin Amurka shi ne nuna goyon baya ga masu tsattsauren ra'ayi na Hong Kong, tare kuma da tsoma baki a cikin harkokin kasar Sin yadda take so, to sai dai kuma kasar Sin na yin adawa da lamarin, kuma ta yi kakkausan suka kan lamarin.

Sharhin ya kuma yi nuni da cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, mazauna yankin Hong Kong sun fita tituna, domin yin shara, tare kuma da kawar da shingayen da masu tsattsauren ra'ayi suka kafa, kana sun yi taro domin nuna goyon baya ga gwamnati da 'yan sandan yankin, ta hanyar daukan hakikanin matakai, amma wasu Amurkawa sun kasa kula da bukatun mazauna Hong Kong, har ma sun kai ga fitar da dokar dake da nasaba da yankin, wannan mataki da suka dauka, ya sabawa yunkurin mazauna yankin, kuma ko shakka babu zai gamu da kiyayya da suka daga wajen daukacin Sinawa, ciki hadda mazauna yankin na Hong Kong, wadanda yawansu ya kai miliyan 7 da dubu 500.

Sharhin ya jaddada cewa, aniyyar gwamnatin kasar Sin ta kiyaye ikon mulki da tsaro, da moriyar ci gaba, ba za ta canja ba, kuma aniyyarta ta aiwatar da ka'idar kasa daya amma tsarin mulki biyu a yankin Hong Kong ba za ta canja ba, kana aniyyarta ta adawa da kasashen waje masu tsoma baki a cikin harkokinta ita ma ba za ta canja ba. Ko shakka babu wasu Amurkawa ba za su cimma yunkurinsu na tsoma baki a cikin harkokin kasar Sin ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China