Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Jawabin shugaban kasar Sin ya nuna inda za a dosa wajen daidaita batun Hong Kong
2019-11-18 14:38:00        cri

 

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shugabannin kasashen BRICS karo na 11 a birnin Brasilia a kwanakin baya, ya fito karara, ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin a kan batun Hong Kong. Inda ya jaddada cewa, kawo karshen tarzoma tare da maido da doka da oda, shi ne aiki na gaggawa kuma na farko da ke gaban Hong Kong, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan hukumar yankin musamman na Hong Kong ta gudanar da mulkinta bisa doka, kuma 'yan sanda su tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata, sa'an nan hukumomin shari'a na Hong Kong ma su hukunta masu laifuka kamar yadda doka ta tanada.

A tsawon watanni biyar da suka gabata, a sakamakon wutar da'yan aware na Hong Kong da wasu gungun mutane daga waje suka rura, masu laifukan nuna karfin tuwo sun toshe hanyoyi tare da barnata kayayyaki da ma kai hari ga'yan sanda a Hong Kong, inda suka keta dokoki da oda da tsari da oda, da kwanciyar hankali da ma ci gaban yankin, sun kuma karya ka'idar kasa daya tsarin mulki biyu da ake aiwatarwa. Al'ummar Hong Kong na tafiyar da harkoki da rayuwa bisa doka. Don haka, ko kadan ba za a yarda da a ci gaba da aikata laifukan take dokoki da kwanciyar hankali da kalubalantar tsarin kasa daya amma tsarin mulki biyu a yankin ba.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China