Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba zai yiwu Amurka ta cimma nasarar tayar da hargitsi a HK ba
2019-11-22 19:36:20        cri

A yau Juma'a ne gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Ba zai yiwu Amurka ta cimma nasarar tayar da hargitsi a yankin Hong Kong ba", inda aka nuna cewa, kwanan baya majalisar dattijai ta Amurka ta zartas da wata doka kan hakkin dan Adam da demokuradiya a yankin Hong Kong na shekarar 2019, domin nuna goyon baya ga masu tsattsauran ra'ayi, wadanda suke aikata laifuffuka a yankin, kuma wannan mataki da ta dauka tsoma baki ne a fili, cikin harkokin gida na kasar Sin, wanda sam ba zai cimma nasara ba.

Sharhin ya bayyana cewa, bisa mataki na farko, wasu 'yan siyasar Amurka suna son kara karfafa zuciyar masu tsattsauren ra'ayi a Hong Kong, domin su ci gaba da aikata laifuffuka, bisa mataki na biyu kuma, suna son yin barazana ga wadanda suke kokarin kiyaye yanayin kwanciyar hankali a yankin, tare kuma da gurgunta ka'idar kasa daya tsarin mulki iri biyu ta kasar Sin. A mataki na uku kuwa, suna son hana ci gaban kasar Sin ta hanyar tsoma baki a cikin harkokin gidanta a yankin Hong Kong.

Sharhin ya kara da cewa, ka'idar kasar Sin ce take kiyaye matsayin tattalin arziki da cinikayya na yankin Hong Kong, kana Sinawa da kansu suna son yin kokari matuka, wajen cimma burin ci gaban kasar, da farfado da al'ummar kasar, da kuma jin dadin rayuwarsu.

Duk wadannan ba su da nasaba da Amurka ko kadan, kuma ana sa ran cewa, wadannan 'yan siyasar Amurka za su daina haifar da barazana, in ba haka ba, illar hakan za ta koma kan su. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China