Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci masu ruwa da tsaki a yankin Hong Kong su yi kokarin dawo da doka da oda
2019-11-19 10:53:53        cri

Mai Magana da yawun zaunanen kwamitin kula da harkokin majalisa na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, Zang Tiewei, ya yi jawabi kan hukuncin da babbar kotun sauraron manyan laifuffuka ta yankin musamman na Hong Kong ta yanke kan karar da aka gabatar a ranar 19 ga wata.

A jiya ne, babbar kotun dake sauraron manyan laififfyka dake yankin musamman na Hong Kong, ta yanke wani hukunci, inda ta gano cewa, wasu tanade-tanaden dokokin gaggawa na yankin, ba su dace da dokar yau da kullum na yankin Hong Kong ba, lamarin da ya sa babu wasu tanade-tanaden da suka dace.

Sai dai wasu wakilai a majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin sun bayyana rashin gamsuwa, yayin da kwamitin kula da harkokin majalisa na majalisar wakilan jama'a kasar Sin, shi ma ya nuna matukar damuwa kan wannan batu.

Kakakin ofishin kula da harkokin yankunan Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Guang, ya bayyana damuwa game da mummunar illar da hukuncin da aka yanke kan sake bibiyar haramcin rufe fuska da kotun ta bayar a yau ka iya haifarwa.

Yang ya ce, za su sanya ido, tare da bibiyar sakamakon abin da zai biyo bayan karar da aka shigar. Yana fatan gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da bangarorin shari'a, za su gudandar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada, su kuma hada kai wajen kawo karshen tashin hankali da ma dawo da doka da oda a yankin.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China