Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar 5G ta Sin za ta kasance a sahun gaba a duniya, in ji ITU
2019-11-22 14:03:29        cri

Jiya Alhamis, babban sakataren kungiyar harkokin sadarwa ta kasa da kasa ta ITU Zhao Houlin ya bayyana cewa, kasar Sin tana gaggauta aikin raya fasahar yanar gizo ta 5G, kuma ya yi imanin cewa, bisa kokarin da kasar take yi da goyon baya da masu kula da wannan aiki na kasa da kasa suka baiwa kasar, tabbas Sin za ta kasance a sahun gaba a duniya a fasahar 5G.

A jiya ne dai, aka bude taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Beijing, a jawabin da ya bayar ta bidiyo, Zhao Houlin ya ce, kamfanonin sadarwa na kasar Sin da kamfanonin kera na'urori na kasar Sin sun ba da gudummawa matuka wajen tsara ka'idoji game da fasahar 5G. Sa'an nan, a fannin raya wannan fasaha da kuma yadda za a yi amfani da fasahar 5G, kamfanonin sadarwa na kasar Sin suna habaka hadin gwiwa a tsakaninsu da sauran sana'o'in da abin ya shafa, lamarin da zai zama abin koyi ga sauran kasashen duniya a lokacin da za su raya fasahar 5G a kasashensu.

Ko shakka babu, fasahar 5G ta kasar Sin za ta yi muhimmin tasiri ga bunkasuwar kasuwannin fasahar 5G na kasa da kasa, da kuma inganta hadin gwiwar Sin da kasashen duniya kan aikin kyautata zaman takewar al'umma ta hanyar raya harkokin sadarwa.

Bugu da kari, malam Zhao ya ce, a halin yanzu, babu wata kasa ita kadai da za ta ci gaba a dukkan fannoni, ya kamata mu karfafa hadin gwiwar bangarorin da abin ya shafa. Haka zalika kuma, akwai bukatar kasashen duniya su hada gwiwa a harkokin raya fasahar yanar gizo ta 5G. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China