Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gina tashar samar da siginar 5G fiye da dubu 50 a bana
2019-08-28 10:42:46        cri

Bikin baje kolin sana'o'in zamani na kasa da kasa na shekarar 2019 ya gabatar da dandalin kolin tattauna sana'ar 5G a jiya Talata, inda jami'in ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, bisa tsarin da aka tsayar, Sin tana shirin gina tashoshin samar da siginar 5G fiye da dubu 50 a birane 50.

An ba da labari cewa, ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta baiwa kamfanonin kasar 4 lasisi na gudanar da aikin sadarwar 5G a ran 6 ga watan Yunin wannan shekara, matakin da ya alamanta cewa, fasahar 5G ta shiga kasuwar kasar Sin. Ya zuwa yanzu, an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata har sana'ar ta rika samun bunkasuwa, kana kuma ana gina yanar gizo ta 5G yadda ya kamata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China