Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin China Mobile yana amfani da fasahar 5G a cibiyoyi 50,000
2019-11-16 16:49:47        cri
Daya daga cikin manyan kamfanonin wayar hannu na kasar Sin wato China Mobile, yana da kusan rassa 50,000 dake amfani da fasahar 5G ya zuwa yanzu, shugaban kamfanin Yang Jie ya bayyana hakan.

Yang yace, a halin yanzu kamfanin yana samar da yanayin sadarwa na 5G a birane 50.

Kamfanin zai cigaba da samar da ingantattun fasahohi kuma zai kaddamar da manhajojin fasahar 5G domin biyan muradun abokan hulda, in ji babban jami'in.

A farkon watan Yuni, kasar Sin ta bayar da lasisin fasahar 5G ta bangaren kasuwanci, hakan ya kawo fara amfani da sabon tsari ga kamfanonin sadarwar kasar.

A cewar kwalejin nazarin fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin, ana sa ran fasahar 5G zata samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 8 nan da shekarar 2030.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China