Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nan da karshen shekara tashoshin 5G a Beijing za su kai 10,000
2019-08-07 20:28:14        cri

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta birnin Beijing, ta bayyana cewa, nan da karshen wannan shekara, ana sa ran gina tashoshin 5G sama da 10,000.

Ya zuwa watan Yuli, an gina sama da irin wadannan tashoshi 7,800 a birnin na Beijing, galibinsu na cikin shiyyoyin birnin, da wuraren bikin baje kolin lambunan shan iska da na gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022, da wajen gundumar Tongzhou.

Karin biranen kasar Sin na kokarin samar da fasahar sadarwar 5G don biyan bukatun jama'a.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China