Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar New York Times tana neman shafa wa jihar Xinjiang kashin kaza
2019-11-20 10:03:48        cri
A kwanakin nan ne, jaridar New York Times ta kasar Amurka, ta wallafa wani rahoto da ta kira na musamman, don ta bata sunan shirin yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da ake gudanarwa a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Jaridar dai, tana ikirarin cewa, ta samu wasu muhimman takardun bayanai, amma ba ta yi karin haske kan yadda aka tattara da ma zabar wadannan takardun ba.

Sanin kowa ne cewa, yada bayanan karya, ya saba tsari da ma ka'idojojin aikin jarida, kana irin wannan danyen aiki na rashin kwarewa, ya nuna yadda wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka dade suna takalar manufofi da ra'ayin kasar Sin, da gangan don su bata sunan kasar Sin.

Da ma an ce doki mai baki ya fi gudu. Sannan duk wasu shaidu da ma tarin karairayin da jaridar za ta baza, hakar ta ba za ta cimma ruwa ba. Domin jihar Xinjiang da ke kokarin farfadowa da samun makoma da zaman lafiya, yana da karfin juri duk wasu karairayi da ma yunkurin neman bata mata suna.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China