Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dangantakar Sin da Afrika na bunkasa ayyukan masana'antu a nahiyar
2019-11-21 09:35:43        cri
Yayin da Afrika ke tsaka da fafutukar bunkasa bangaren masana'antu, kwararru daga ciki da wajen nahiyar sun yabawa taimakon da kasar Sin take ba nahiyar.

Da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Laraba, Arancha Gonzalez, Daraktar Zartarwa ta cibiyar cinikayya ta kasa da kasa ITC, ta ce kara shigar kasar Sin nahiyar Afrika da sha'awar da ta ke da shi kan damarmakin da nahiyar ke da su na bunkasa ayyukan masana'antu a nahiyar.

Darktar wadda ta ce kasar Sin ta mayar da hankali sosai kan ayyukan masana'antu a Afrika, ta bayyana haka ne a gefen taron da aka yi domin ranar masana'atu ta nahiyar, da aka yi jiya a hedwatar hukumar AU dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

An gudanar da bikin ranar masana'atu ta nahiyar Afrika ne a wani bangare na makon raya masana'atun nahiyar na 2019, wanda ke gudana daga ranar 18 zuwa 22 ga wata. Makon na kuma jaddada irin muhimmiyar rawar da yankunan masana'antu da na cinikayya mara shinge za su taka wajen bunkasa bangaren masana'atu a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China