Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana dora muhimmanci kan raya alaka da Guinea
2019-11-19 10:25:32        cri
Mataimakin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, Wu Weihua, ya bayyana cewa, kasarsa tana dora muhimmanci matuka kan raya alaka da kasar Guinea, tana kuma fatan bude wani sabon babin abokantaka da kasar.

Wu, ya kuma yi kira da a yi amfani da damammakin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya, da aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing a watan Satumban shekarar da ta gabata, don yayata gina al'umma mai kyakyawar makoma tsakanin kasar Sin da Guinea da ma al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afirka.

Babban dan majalisar zartarwar ya bayyana hakan ne yayin ziyarar kwanaki uku da ya kammala jiya Litinin a kasar ta Guinea, inda ya gana da shugaban Guinea Alpha Conde da firaministan kasar Ibrahim Kassory Fofana, daga bisani ya tattauna da kakakin majalisar dokokin kasar Clause Kondiano.

Yayin ganawa jagororin kasar, sun yi bayani sosai kan nasarorin da aka cimma karkashin hadin gwiwarsu, tun lokacin da kasashen Sin da Guinea suka kulla dangantakar diflomasiya a shekarar 1959, tare da yaba kudirin kasar Sin, kan manufofinta na ketare na zaman lafiya, suna masu yaba kasar ta Sin kan yadda ta ke nuna wa kasashen Afirka dabarun raya kasa da za su dace da yanayin kasashensu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China