Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana kudurinta na mara baya ga gwamnatin riko ta Sudan
2019-10-28 11:20:38        cri
MDD ta bayyana kudurinta na mara baya ga gwamnatin riko na Sudan, wajen kafa demokradiyya da farfado da tattalin arziki da zaman lafiya.

Sudan da MDD sun yi bikin ranar MDD na bana a jiya Lahadi a birnin Khartoum. Ranar MDD, rana ce da kundin tsarin MDD ya fara aiki a shekarar 1945.

Da take jawabi, mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina Jane Mohammed, ta bayyana kuduri da goyon bayan majalisar ga firaministan Sudan Abdalla Hamdok, la'akari da yadda gwamnatin ke damawa da mata da matasa a dukkan wasu muhimman ayyukan raya kasa.

Ta ce Sudan na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yanki. Tana mai cewa nasarar Sudan, nasara ce ta MDD.

A nasa bangaren, sakataren ma'aikatar harkokin wajen Sudan, Siddiq Abdul-Aziz, ya bayyana kudurin gwamnatin kasar na kiyaye tsarin shugabanci na gari da dokoki da kuma dora kasar kan turbar demokradiyya da farfado da tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China