Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan da 'yan adawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin taron tattaunawa
2019-10-22 10:26:44        cri
Gwamnatin Sudan da gamayyar kungiyoyin 'yan adawa masu fafutukar kwatar 'yancin Sudan a ranar Litinin sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi 8 na zaman lafiyar kasar a Juba, babban birnin Sudan ta kudu gabanin fara taron tattaunawar siyasar kasar.

Mohamed Al-Hassan Al-Taishi, mamban majalisa mai cin gashin kanta ta Sudan, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, sanya hannu kan yarjejeniyar siyasa da kuma yarjejeniyar tsakaita bude wuta a yankuna da ake fama da tashe-tashen hankula alamu ne dake nuna cewa ana samun nasarori a shirin ajandar wanzar da zaman lafiyar kasar.

Kungiyar Sudanese Revolutionary Front ta kunshi kungiyar fafutukar tabbatar da adalci ta kasar wato Sudan's Justice and Equality Movement, da kungiyar Sudan Liberation Movement (SLM) /Minni Minnawi da Sudan People's Liberation Movement (SPLM)/arewaci da kuma sauran kungiyoyin fafutuka daga yankin arewaci da gabashin Sudan.

Tun a ranar 14 ga watan Oktoba ne, birnin Juba yake karbar bakuncin tarukan tattaunawa tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyin masu dauke da makamai daga yankin Darfur, da kudancin Kordofan da kuma shiyyar Blue Nile. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China