Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba ta fuskantar yanayin hauhawa da faduwar farashin kayayyaki
2019-11-16 17:00:11        cri
Babban bankin kasar Sin ya ce kasar ba ta fuskantar yiwuwar ci gaba da samun faduwa ko hauhawar farashin kayayyaki, domin manufofin gwamnati kan harkokin tattalin arziki na aiki yadda ya kamata.

Babban bankin ya bayyana cikin rahoton da yake fitarwa a kowanne rubu'i cewa, tattalin arzikin kasar a cikin gida na fuskantar matsi, kuma ya kamata a kara karfafa yadda yake tafiya.

Rahoton ya ce babban bankin zai matse kaimi wajen aiwatar da dabarun tinkarar yanayin da tattalin arzikin ke ciki, yayin da kuma za a kaucewa amfani da manufofin inganta saurin karuwa.

Bankin ya ce ya kamata a inganta kare yaduwar tsammanin samun hauhawar farashin kayayyaki a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China