Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya gana da mataimakin gwamnan jihar Kano
2019-11-13 20:38:48        cri

Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya gana da mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna, inda suka yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi kyakkyawar hadin kai a tsakanin kasashen biyu, da mu'amala a tsakanin kananan hukumomin sassan biyu.

A yayin ganawar, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi bayani game da ziyarar da ya kai a lardin Shandong na kasar Sin, a cewarsa, Allah ya albarkaci jihar Kano da yawan al'umma, da albarkatu, tana kuma da makomar bunkasuwa a nan gaba, wadda ta kasance wurin da kamfanonin kasar Sin ki ribibin zuwa a arewacin Najeriya. Ya ce, jiharsa na son kara kyautata yanayin zuba jari, da nufin kara jawo hankulan kamfanonin kasar Sin don su zuba jari a jihar, ta yadda za a cimma burin samun moriya da nasara tare.

A nasa bangaren, jakada Zhou Pingjian ya nuna godiya ga gwamnatin jihar Kano kan yadda ta saukaka Sinawa dake jihar a fannonin gudanar da ayyuka da ma zama a wurin, ya kuma bayyana cewa, yin cudanya da hadin kai a tsakanin kananan hukumomi, wani muhimmin sashe ne na kyakkyawan hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Najeriya, kasar Sin na fatan karfafa cudanya da hadin kai tare da bangaren Najeriya a fannonin samar da kayayyaki, al'adu, yawon shakatawa, aikin gona da kuma masana'antun kere-kere, kana ya bayyana fatansa na ganin Najeriya ta kara kyautata muhallin gudanar da cinikayya, don kara jawo hankulan masu zuba jari na kasar Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China