Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya na goyon bayan a daidaita hargitsi a HK
2019-11-17 20:58:09        cri

Yanzu haka ana maida hankali matuka kan muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar kan yanayin da yankin Hong Kong ke ciki, mutanen fannoni daban daban a fadin duniya sun bayyana cewa, suna goyon bayan gwamnatin kasar Sin, kuma suna sa ran za ta maido doka da oda a yankin cikin sauri.

Masanin harkokin kasar Sin na kasar Jordan kuma marubutun littafi Samir Ahamd yana ganin cewa, a cikin jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nacewa ka'idarta ta kasa daya amma tsarin mulk iri biyu a yankin Hong Kong, ta yadda za a cimma burin wato mazauna yankin suna tafiyar da harkokin yankin, a sa'i daya kuma suna jin dadin damammakin ci gaban da babban yankin kasar ke samarwa, ka'idar nan ta nunawa kasa da kasa dabarun siyasar kasar Sin masu hikima, ita ma ta samu amincewa daga wajen al'ummomin kasashen duniya.

Darektan cibiyar nazarin shawarar ziri daya da hanya daya ta Serbia Yvona Rajewatts ta bayyana cewa, kasar Sin za ta mayar da martani kamar yadda ta yi bisa doka, domin gudanar da harkokin kasa cikin lumana, ko shakka babu za ta ci gaba da aiwatar da ka'idar kasa daya tsarin mulki iri biyu a yankin Hong Kong, tare kuma da kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa da moriyar al'ummun kasarta yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China