Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin Shugaba Xi Ya Kara Imani Da Nuna Kyakkyawar Makoma Ga Yankin Hong Kong
2019-11-17 21:10:25        cri
A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin game da yanayin yankin Hong Kong a yayin da yake halartar taron koli na kungiyar BRICS a kasar Brazil. Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da suka tsananta a yankin Hong Kong sun kawo illa ga tsarin dokoki da odar zamantakewar al'umma, da zaman lafiya da na karko a yankin, da kuma keta ka'idojin tsarin kasa daya amma da tsarin mulki biyu. Mutane daga bangarori daban daban na yankin Hong Kong sun bayyana cewa, jawabin shugaba Xi ya shaida imanin gwamnatin kasar Sin na tabbatar da ikon mallaka da tsaro da kuma moriyar bunkasuwa, wanda zai jagoranci jama'ar bangarori daban daban na yankin da su hada kai don nuna goyon baya ga gwamnatin yankin wajen dakatar da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

A ganin bangarori daban daban na yankin Hong Kong, ayyukan masu tsattsauran ra'ayin sun tsananta, wadanda suke da alamar harin ta'addanci. Game da hakan, tilas ne gwamnatin yankin ta kafa rukunin daidaita rikici, wanda ya hada da albarkatun hukumomi daban daban na gwamnatin don dakatar da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da mayar da odar zamantakewar al'ummar yankin. Ya kamata bangarori daban daban su tinkarar da batun da nemi cimma daidaito don yin kokari tare wajen tabbatar da tsaron yankin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China