Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar kasa daya amma da tsarin mulki biyu
2019-11-17 20:35:12        cri
A yayin ganawa ta 11 a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS da aka yi a Brasilia, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da suka tsananta a yankin Hong Kong sun kawo illa ga tsarin dokoki da odar zamantakewar al'umma, da zaman lafiya da na karko a yankin, da kuma keta ka'idojin tsarin kasa daya amma da tsarin mulki biyu. Wadannan fannoni uku sun nuna babbar illa da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi suka kawo, da kuma shaida wa kasa da kasa hakikanin yanayin da ake ciki a yankin Hong Kong.

An yi nuni da cewa, jawabin shugaba Xi Jinping ya shaida ra'ayin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin na dakatar da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi a yankin Hong Kong, babu shakka yankin Hong Kong zai samu kyakkyawar makoma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China