Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta amince da yunkurin kin yarda da ka'idar kasa daya tsarin mulki biyu a HK ba
2019-11-17 20:51:35        cri

A gobe Litinin 18 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin za ta wallafa wani sharhi mai taken "Kasar Sin ba za ta amince da yunkurin kawo barazana ga ka'idar kasa daya tsarin mulki iri biyu a yankin musamman Hong Kong ba".

Sharhin ya bayyana cewa, yayin ganawa karo na 11 dake tsakanin shugabnanin kasashen mambobin kungiyar BRICS a kasar Brazil, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi kan yanayin da yankin Hong Kong ke ciki yanzu, inda ya yi nuni da cewa, ayyukan nuna karfin tuwo da masu tsattsauren ra'ayi suke yi a yankin suna kawo babbar barazana ga ka'idar kasar Sin a yankin wato kasa daya amma tsarin mulki iri biyu, kasar Sin ba za ta amince da yunkurin ba, dole ne a hukunta masu aikata laifuffuka bisa doka.

Sharhin ya kara da cewa, idan aka kawo barazana ga ka'idoji uku na kasar Sin wato kawo illa ga tsaron kasa, da kawo barazana ga ikon mulkin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da babbar dokar yankin Hong Kong, da kuma kawo barazana ga babban yankin kasar Sin ta hanyar gudanar da ayyukan karfin tuwo a yankin Hong Kong, ba zai yiyu ba su cimma yunkurinsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China