Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoffin 'yan siyasar kasashe da dama sun goyi bayan matsayar kasar Sin tare da kira da a dakatar da rikici a HK
2019-11-19 10:23:30        cri
Biyo bayan ayyukan masu tsattsauran ra'ayi a yankin HK a baya-bayan nan, tsoffin shugabannin gwamnatocin kasashen waje, sun bayyana goyon bayansu ga manufar gwamnatin kasar Sin ta "kasa daya mai tsarin mulki biyu" tare da adawa da katsalandan cikin harkokokin HK daga kasashen waje, suna masu kira da a kawo karshen rikici da tashin hankali a yankin.

Cikin watanni 5 da suka gabata, masu tsattsauran ra'ayi dake zanga-zanga, sun lalata kayayyakin gwamnati tare da keta dokoki, har ma da illata mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya bazu zuwa cikin makarantun yankin. Tsoffin 'yan siyasar na kasashe da dama, sun kadu da irin wadannan munanan ayyukan. Galibin tsoffin shugabannin sun damu da yanayin da daliban kasashen wajen ke ciki a yankin, tare kuma da yabawa da kwarewa da juriya irin na 'yan sandan HK. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China