Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin gwamnan yankin Hong Kong ya tuhumi kalaman Sanatan Amurka kan masu bore
2019-10-14 13:26:16        cri
Ofishin gwamnan yankin musamman na Hong Kong (HKSAR), ya sanar a jiya Lahadi cewa, kalaman da sanatan Amurka Ted Cruz yayi, inda yace bai ga wani tashin hankali da masu zanga zanga suka yi ba kalamai ne na ruruta wutar rikici.

Kakakin ofishin na HKSAR ya ce, duk da kasancewar suna mutunta 'yancin fadin albarkacin baki ga 'yan siyasar kasashen ketare, amma tilas ne a bayyana ra'ayi bisa tushen gaskiya ta kwararan hujjoji.

Rikici ya barke a 'yan watannin baya a Hong Kong yayin masu bore suka lalata kayayyakin tashoshin jiragen kasa, da cinna wuta a shaguna, da kaddamar da hare hare da abubuwan fashewa kan jami'an 'yan sanda da kuma dukan jama'a mazauna yankin dake da sabanin ra'ayin siyasa da masu boren.

Kakakin ya sanar cewa, kowa ya gani a cikin rahotannin da kafafen yada labarai suka nuna yadda masu zanga zangar ke tada hankula, da lalata kayayyakin gwamnati a lokuta da dama a Hong Kong cikin 'yan watannin da suka wuce.

Sanarwar ta ce, kafin su bayyana ra'ayoyinsu, ya kamata 'yan siyasar kasashen waje su yi kwatanta irin abin da za su yi idan al'amarin a kasashensu ya faru, a maimakon su dinga sukar lamirin Hong Kong ba tare da girmamawa ba, ko kuma su dinga goyon bayan ayyukan tashe tashen hankula.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China