Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin Hongkong ta yi Allah wadai da aikace-aikacen nuna karfin tuwo
2019-09-22 16:08:38        cri
Kakakin gwamnatin yankin musamman na Hongkong na kasar Sin, ya yi Allah wadai da masu zanga-zangar da suka keta doka gami da aikace-aikacen nuna karfin tuwo a Tuen Mun, da wasu ungwanni na Hongkong.

A cewar kakakin, bayan kammala zanga-zanga a unguwar Tuen Mun a jiya, sai wasu suka fara daukar matakan nuna karfin tuwo gami da lalata dukiyoyin jama'a, inda suka toshe hanyoyi, da kunna wuta, da jefa wasu abubuwan fashewa masu kunshe da man fetur, lamarin da ya zama barazana ga tsaron 'yan sanda da jama'ar dake wurin. Ban da haka, wasu daga cikinsu sun yi wa 'yan sandan dake sintiri a wurin duka, gami da neman kwace bindigogi daga hannun 'yan sandan, har ma wusu sun taka tare da kona tutar kasa, inda suke takalar hukuma ta hanyar keta mulkin kan kasa.

Dangane da wadannan ayyuka, kakakin ya ce 'yan sandan Hongkong za su dauki kwararan matakai don gurfanar da wadanda suka keta doka a gaban kuliya, don tabbatar da tsaron al'umma, da maido da doka da oda. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China