Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Burtaniya da ta kama wadanda suka kaiwa wata jami'ar yankin Hong Kong hari
2019-11-15 20:32:37        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya shaidawa taron manema labarai da aka gudanar a yau Jumma'a cewa, kasar sa ta nuna matukar bacin rai da ma Allah wadai da harin da aka kaiwa darektar harkokin shari'a ta yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a Burtaniya.

Don haka, kasar Sin ta bukaci bangaren Burtaniya, da ya gaggauta gudanar da bincike kan lamarin, ya kuma yi kokarin damke wadanda suka aikata wannan danyen aiki, don a gurfanar da su a gaban kuliya.

A jiya ne dai, wasu mutane da suka rufe fuskokinsu, suka kaiwa Zheng Ruohua, sakartariyar sashen shari'a ta yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin hari, lokacin da take halartar wani biki a London har ta ji rauni. Yanzu haka tana samun kulawa a asibiti. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China