Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayar da katin bankuna sama da biliyan 7
2019-06-24 10:46:05        cri

Kimanin katin bankuna biliyan 7.83 kasar Sin ta bayar ya zuwa karshen shekarar 2018, inda kowane Basine ya samu katin banki kusan 0.7 na shigar da kudi sanann na cire kudi 4.92.

Hada-hadar cinikin da aka gudanar da katinan sun kai yuan tiriliyan 789.6 kwatankwacin dala tiriliyan 114.61, inda hakan ya nuna cewar an samu karuwar adadin cikin yanayi mai kyau, inji rahoton da kungiyar bankunan kasar Sin ta sanar.

Cikakken bayanin ya nuna cewa, kasar Sin ta bayar da katin shigar da kudi kimanin miliyan 970 inda adadin hada hadar da aka gudanar ya tasamma yuan tiriliyan 38.2, yayin da katinan cire kudi ya kai biliyan 6.86 inda aka yi hada hadar yuan tiriliyan 751.4.

Bisa ga yanayin cigaba da karuwar kasuwanci ta hanyar amfani da katin bankuna, kasuwar amfani da katunan tana cigaba da samun karbuwa cikin sauri, inji rahoton.

Katin biyan kudi mafi girma na kasar Sin wato Union pay ya kara fadada harkokin kasuwancinsa zuwa kasashe da shiyyoyin duniya kimanin 171. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China