Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawancen Sin da Afrika ya taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka in ji wata jami'ar AU
2019-08-23 09:43:45        cri
Mai ba da shawara ga shugaban kungiyar AU a fannin cinikayya Rossette Nyirinkindi Katungye, ta ce akwai bukatar kasashen Afirka su yi kokarin cin cikakkiyar gajiya daga kawancen su da kasar Sin, ta yadda za su karfafa fannonin su na fasaha, da sanin makamar aiki a bangaren masana'antu, tare da ingiza ci gaban nahiyar baki daya.

Rossette Nyirinkindi Katungye, ta yi wannan tsokaci ne yayin zantawar ta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron da aka gudanar a birnin Accra, game da yarjejeniyar kafa yankin cinikayya maras shinge na Afirka ko AfCFTA a takaice.

Jami'ar ta ce Sin ta zamo wata babbar dama ta samun horo a fannonin raya cinikayya, da masana'antu, da kasuwanci da ma wasu sauran sassa da za su taimakawa ci gaban nahiyar Afirka.

Game da alfanun dake tattare da fara aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA kuwa, Katungye ta bayyana burin ganin kasashen Afirka sun yi amfani da kudadensu, yayin da suke gudanar da hada hadar cinikayya, wanda hakan zai bunkasa harkokin cinikayya da kasuwanci a sassan nahiyar.

Ta ce ko shakka babu yarjejeniyar ta aza tubulin inganta cudanya tsakanin kasashen nahiyar Afirka, don haka babu wani dalili da zai sanya kasashen su zauna a bar su a baya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China